July 31, 2021

‘Yan Bindiga: Sun kashe Sarkin Tauri tare da wani mutum 1 a Katsina

2 min read
Yan bindiga

Wasu 'yan bindiga sun kashe wani dattijo mai shekaru 50 mai suna Ashiru Aliyu a sa'o'in farko na ranar Litinin a kauyen Daulai da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani dattijo mai shekaru 50 mai suna Ashiru Aliyu a sa’o’in farko na ranar Litinin a kauyen Daulai da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Kamar yadda jaridar Katsina Post ta wallafa, ‘yan bindigar sun sace mata masu yawa, sun kwashe dabbobi masu tarin yawa tare da kwashe kayayyakin abinci yayin harin.

‘Yan bindigar sun isa kauyen wurin karfe 1:00 na dare kuma sun fara harbe-harbe babu kakkautawa.

A nan ne aka tabbatar da sun kashe rayuka biyu a take.

Hakazalika, wadanda ake zargin ‘yan bindigar dajin ne, sun kashe wani basarake mai sarautar Sarkin Tauri na garin Dandume tare da garkuwa da wasu mutane hudu da suka hada da matan aure.

  Atiku Abubakar yayi niyyar mayarda 'ya-'yan su 3 ga tsohuwar matarsa

Lamarin ya faru wurin karfe 2 na daren ranar 14 ga watan Satumba, kamar yadda Katsina Post ta wallafa.

Daya daga cikin mazauna yankin ya ce, ‘yan bindigar da suka tsinkayi garin sun kai 30.

An gano cewa wasu daga cikin mazauna kauyen sun tsere harin ta hanyar fadawa daji tare da sauran yankunan da ke da kusanci da su.

Katsina: ‘Yan bindiga sun kashe dagaci da wani mutum 1, sun sace mutane masu yawa

  Najeriya: Hanyoyin samun tallafin gwamnatin Bubari a saukake

Katsina: ‘Yan bindiga sun kashe dagaci da wani mutum 1, sun sace mutane masu yawa. Hoto daga Sahara Reporters

A wani labari na daban, wasu ‘yan bindiga sun kwashe wasu matafiya da ke kan babbar hanyar Jibia zuwa Gurbi ta jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da su zuwa inda babu wanda ya sani.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta gano, a yayin da suke kan hanyar shiga daji da matafiyan, direban yayi yunkuri tserewa inda a take suka harbeshi suka bar shi a nan.

  Inna lillahi: Kimanin sojoji goma 'yan ta'adda suka kashe Najeriya yau dinnan

Majiyar ta kara da cewa, wasu mazauna kauyen ne suka tsinci direban bayan kwanaki biyu da aukuwar lamarin.

A nan ya sanar da jama’ar cewa, a kalla mutu 20 ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su. A halin yanzu yana asbiti inda yake karbar taimakon likitoci.

A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma yace mutum tara kacal aka sace.

Leave a Reply

Translate »