August 3, 2021

Wani dalibi me shekaru 20 kachal ya auri mata biyu a lomaci daya

2 min read
Wani dalibi

Wani dalibi matashi mai shekaru 30 da haihuwa ya auri mata biyu cikin wata guda a kasar Indonesia

Wani dalibi matashi mai shekaru 30 da haihuwa ya auri mata biyu cikin wata guda a kasar Indonesia

Rahotanni sun ce dukkansu matan biyu da ya aura ba su wuce ‘yan shekaru (16) goma sha shida ba

Mahaifin yaron ya ce ya yi mamakin jin dansa zai auri mata biyu duk da cewa yana makaranta amma ya yi alkawarin tallafa musu

Wani dalibi mai shekaru 20 ya auri mata biyu cikin wata guda a West Lombok da ke yankin West Nusa Tenggara a kasar Indonesia.

An rawaito cewa anyi bikin nasu ne cikin shagulgulan gargajiya da da akafi sani da “nikah siri”. 

  Karshen yan SARS ya kare a Najeriya
Dalibib da ya auri mata biyu a shekara 20 tareda matan nasa

Dukkanin amaren basu wuce shekara sha shida (16) ba.

Hotunan auren R da M sun dunga yawo a dandalin sada zumunta ta Facebook wanda hakan ya zama maudu’in da ake tattaunawa a tsakanin masu amfani da yanar gizo.

Da yake bayyanawa wata kafar yada labarai, Kumparan, mahaifi a wajen angon, 

Ya bayyana cewa ya yi mamakin gano cewa ɗan nasa nada sha’awar aure, 

Musamman ganin cewa har yanzu dalibi ne a makarantar gaba da sakandire ta koyon sana’o’i.

“Eh, nayi mamaki. Saboda har yanzu bai kammala makaranta ba. 

  ASUU: An ba hammata isja a taron kawo karshen yajin aiki da FG

Kuma gab ake da rubuta jarrabawar kasa,” mahaifin nasa ya bayyana.

R da M sun kai kimanin shekaru uku suna soyayya, amma R da F sunyi soyayya ne ta ɗan ƙaramin lokaci. 

Bayan da R ya auri F, sai M da iyalinta suka kai ziyara zuwa gidansu R don tattaunawa da iyayensa, inda anan suka nemi R da ya auri ƴarsu M.

Duk da R, F, da M basu yi magana da wata kafa ba dan gane da auren nasu, iyayen R sun nuna a shirye suke da suyi magana da manema labarai.

Ayuni, yayi korafin cewa zai kashe kudin da yakai miliyan 50, sai dai ya bayyana cewa yana da kyakkwawan zaton ɗan nasa zai ci gaba da karatunsa.

  SMEDAN: Yanda Za'a shiga tsarin a saukake--daga buhu se tukunya

“Ina so ɗana ya ci gaba da makarantarsa. Ina da halin da zanci gaba da daukar nauyin karatunsa. 

Zan iya dauke masa bukatunsa na rayuwa. Kuma zan iya daukar nauyin matansa guda biyu,” Ayuni ya bayyana.

Nurminah, mahaifiyar R tana fatan abin da mahaifin nasa yake da, tana fatan cewa auren mata biyu bazai kawo tsaiko ga kammaluwar karatunsa ba.

Leave a Reply

Translate »