August 3, 2021

PDP da ZLP Sun Kalubalanci Gwamna Akeredolu Na APC bisa Zaben Ondo

2 min read
PDP

Jama'ar jihar Ondo yan PDP da ke kudu maso yammacin Najeriya sun kada kuri’a domin zaben gwamnan da zai shugabanci jihar cikin shekara hudu masu zuwa.

Jama’ar jihar Ondo yan PDP da ke kudu maso yammacin Najeriya sun kada kuri’a domin zaben gwamnan da zai shugabanci jihar cikin shekara hudu masu zuwa.

Zaben na ranar Asabar na zuwa ne kasa da wata guda bayan wanda aka yi a jihar Edo a kudu maso kudancin Najeriyar, wanda PDP ta lashe.

Ma biya jamaiyar PDP manya na jihar Ondo na mayarda martani akan Zaben da ya gudana ba da dadewa ba

A wannan zabe mai ‘yan takara 17, gwamna mai-ci Rotimi Akeredolu na jam’iyyar APC, na neman wa’adi na biyu yayin da manyan ‘yan adawa EyitayoJegede na Jam’iyyar PDP da kuma Agboola Ajayi na jam’iyyar ZLP ke kalubalantarsa.

  Wani dalibi me shekaru 20 kachal ya auri mata biyu a lomaci daya

Tsokachi daga Kafafen yada labarai

Wakilin Muryar Amurka Hassan Umaru Tambuwal da ya yi hira da wasu mazauna birnin Akure da wasu sassan jihar ta wayar tarho, ya ruwaito cewa, an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Ko da yake, wasu kafofin yada labaran kasar sun ce an dan samu ‘yar hatsaniya a karamar hukumar Akure ta Kudu, lamarin da har ya kai ga harba bindiga, amma hukumomin tsaro sun ce babu wanda ya ji rauni.

Wani me bada jawaban yanda zabe ya kasance, na tada jijiyar wuya akan aikin zaben

Sannan akwai rahotanni da ke nuna cewa wasu jam’iyyu na zargin an tafka magudi a zaben.

  Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sukai awon gaba da mutane 17 a jahar Nassarawa

Hakan na nufin ba kamar yadda aka saba ganin yadda manyan jam’iyyun kasar biyu suke mamaye zabuka ba, a zaben jihar ta Ondo manyan jam’iyyu uku ne suke gwada kaiminsu.

A zaben 2016, gwamna Akeredolu na APC da Mr. Ajayi na jam’iyyar Zenith Labour Party, (ZLP) wanda shi ne mataimakin gwamna Akeredolu, sun ka da Mr Jegede na jam’iyyar PDP.

Amma Ajayi, ya raba gari da gwamna Akeredolu inda ya sauya sheka ya koma ZLP a wannan zabe don kalubalantar tsohon maigidansa.

Rahotanni sun ce tun da misalin karfe 8:30 na safe aka bude rumfunan zabe da dama a sassan jihar ta Ondo mai kananan hukumomi 18.

  Yawancin mutanen da suka mutu sakamakon zanga-zangar EndSARS a jiya

A kuma lokacin hada wannan rahoto, an rufe da yawa daga cikin rumfunan zaben.

Wannan shi ne karo na biyu da manyan jam’iyyun kasar biyu, wato APC da PDP suke gwada farin jininsu a zaben jihohi wanda wasu masu fashin baki ke cewa zai iya zama manuniya ga abin da zai faru a zaben 2023.

A ranar 19 ga watan Satumba, gwamna mai ci Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP ya lashe zaben jihar ta Edo bayan da ya kada abokin karawarsa Osagie Ize-Iyamu na APC.

Saurari cikakken rahoton Hassan Umaru Tambuwal wanda ya tattaro ra’ayoyin wasu mazauna jihar ta Ondo:

Zaku iya karanta asalain Labarin daga sashen VOA Hausa Dake kasar Amurka, Ta hanyar latsa nan

Leave a Reply

Translate »