August 1, 2021

Inna lillahi: Kimanin sojoji goma ‘yan ta’adda suka kashe Najeriya yau dinnan

2 min read
Inna lillahi

Inna lillah! mayakan ISWAP sun kashe dakarun sojojin Najeriya goma a garin Marte da ke yankin tafkin Chadi

Inna lillah! mayakan ISWAP sun kashe dakarun sojojin Najeriya goma a garin Marte da ke yankin tafkin Chadi

Majiyoyi sun bayyana cewa tawagar motocin sojin na a hanyarsu na kai wa dakarun da ke yankin kayayyakin amfani lokacin da mayakan suka kai masu harin bazata

Har ila yau sojoji takwas sun jikkata a harin

Mayakan ta’addanci masu ikirarin jihadi sun halaka dakarun sojojin Najeriya 10 a wani harin bazata da suka kai kusa da garin Marte da ke yankin tafkin Chadi, wasu majojin tsaro biyu suka bayyana a ranar Laraba.

  'Yan Bindiga: Sun kashe Sarkin Tauri tare da wani mutum 1 a Katsina

Mayakan ISWAP dauke da bindigogin toka da kananan bama-bamai a ranar Talata, sun budewa wata tawagar sojoji wuta a hanyarsu na rabon kayayyaki, jaridar The Guardian ta ruwaito.

“Yan ta’addan sun kashe sojoji 10, ciki harda manyan jami’ai biyu, a harin bazatan,” daya daga majiyoyin taa sanar da AFP.

Hakazalika majiyar ta bayyana cewa sojoji takwas sun jikkata a harin.

Tawagar na a hanyarsu na zuwa kai wa dakarun sojin da ke yankin abinci da sauran kayayyaki lokacin da aka kai masu hari, in ji majiyar wacce ta nemi a boye sunanta.

  Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sukai awon gaba da mutane 17 a jahar Nassarawa

An kuma tattaro cewa yan ta’addan sun sace kayayyakin sannan suka sanya wa manyan motoci biyu wuta kafin suka tsere cikin jeji.

Sun bayyana cewa harin na iya zama ramuwar gayya ga tayar da sansanin yan ta’addan da aka yi a yankin Marte, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mambobinsu da dama, ciki harda kwamandoji uku.

Mayakan ISWAP dai sun balle ne daga Boko Haram a 2016.

A gefe guda, mun ji cewa kwamishinan shari’a na jihar Borno, Kaka Lawan, ya yi bayanin yadda mayakan Boko Haram suka kai wa gwamnan jihar, Babagana Zulum hari.

  ASUU: An ba hammata isja a taron kawo karshen yajin aiki da FG

Lawan ya ce an fara kai wa gwamnan hari ne da abubuwan fashewa da aka dasa a hanyar da tawagarsa za su bi, sannan ya ce an kai hari na biyu ne ta hanyar daura wa jaki bam.

Yan ta’addan Boko haram sun kai wa Zulum wasu hare-hare mabanbanta har guda biyu cikin yan kwanakin da suka gabata.

Leave a Reply

Translate »