Gwamnatin tarayya ta gargadi matasa da suyi rijistan NYIF don Cigabansu
1 min read
Gwamnatin janar Buhari wati Gwamnatin tarayya na kokarin dagewa wurin tallafawa matasa da jari musamman masu kananan sana'o'i don rage rashin aikin yi a Najeriya
Gwamnatin janar Buhari wati Gwamnatin tarayya na kokarin dagewa wurin tallafawa matasa da jari musamman masu kananan sana’o’i don rage rashin aikin yi a Najeriya
Daya daga cikin manyan hadimomin Shugaban kasa Buhari na musamman, wato Lauretta Onochie ta sanar da hakan a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter
Ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta saki adireshin yanar gizo wadda matasan da basu wuce shekaru 18 zuwa 35 ba zasu bi su samu tallafin
FG na kokarin rage rashin aikin yi a Najeriya, inda ta bayar da adireshin yanar gizo da matasa zasu samu damar samun jari, don tallafawa masu kananan sana’o’i.
Laureta Onochie ta sanar da hakan a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba ta kafar sada zumuntar zamani.
Abinda ya dade ne domin kuwa dama ministan matasa da bunkasa wasanni, Sunday Dare, ya sanar da amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari da bayar da naira biliyan 75 don tallafawa matasa.
Ya jaddada cewa za’ayi aikinne na tsawon shekaru 3, a kowacce shekara za’ayi amfani da naira biliyan 25, kamar yadda shugaban kasar ya amince.
Hadimar ta kara da cewa, “gwamnatin tarayya ta saki adireshin yanar gizo ta shirin NYIF don tallafawa sana’ar matasa masu shekaru 18 zuwa 35.”