July 31, 2021

FG ta gabatar da manhajar UTAS kuma sun bayyana cewa suna dab da samun masalaha tsakaninsu da ASUU

2 min read
UTAS

Za a gabatar da UTAS a gaban AGF, NITDA, da NSA kafin a amince da manhajar

Za a gabatar da UTAS a gaban AGF, NITDA, da NSA kafin a amince da manhajar

A ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, 2020, gwamnatin tarayya ta ce ta na duba yiwuwar karbar manhajar UTAS da kungiyar ASUU ta gabatar.

Kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta gabatar da UTAS a gaban gwamnatin tarayya, a matsayin madadin manhajar nan ta IPPIS ta biyan albashin.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi la’akari da abin da ASUU ta zo da shi. 

  Najeriya: Hanyoyin samun tallafin gwamnatin Bubari a saukake

Wannan sanarwa ya fito ne daga bakin Ministan kwadago, Dr. Chris Ngige.

Jaridar Premium Times ta bayyana cewa Chris Ngige ya bayyanawa ‘yan jarida wannan ne bayan zaman sa’a biyu da ASUU ta yi da majalisar dattawa.

Asuu da fg

Ngige ya ce a nan gida aka kirkiro manhajar da aka zo da shi, don haka ta cancanci a jarraba ta.

  Atiku Abubakar yayi niyyar mayarda 'ya-'yan su 3 ga tsohuwar matarsa

“Mun yarda bayan taron cewa mu yi la’akari da UTAS da aka zo da shi a madadin dabbakar da manhajar IPPIS da ke ta kawo mana matsaloli.” Inji sa.

Ngige ya ce: “Ba mu yi watsi da IPPIS gaba daya ba, kuma ba mu karbi UTAS kaco-kam ba.”

“Matsayar da mu ka kai ita ce mu yi wa manhajar ASUU binciken tsa-tsaf. 

  Munirat Abdulsalam ta bayyana kasancewarta musulma

Za a gabatar da UTAS a ofishin babban akawun gwamnatin Najeriya a Laraba.”

Ministan ya ce daga nan za a kai wa NITDA manhajar domin ta duba, sai kuma a tafi NSA.

Bayan zaman da aka yi, Ahmad Baba Kaita ya tabbatar da cewa ana neman kai ga maslaha

Leave a Reply

Translate »