August 3, 2021

EndSARS: Kimanin mutane 10 na masu zanga-zanga yansanda suka kashe

2 min read
EndSARS

Zanga-Zangar tsige SARS

Yan sanda sun kashe masu zanga zangar EndSARS guda 10 – Amnesty

Taura Kungiyar Amnest International, ta ce rundunar ‘yan sanda sun kashe mutane 10 da ke zanga zangar #EndSARS da aka fara ranar Alhamis.

Zanga-Zangar tsige SARS

Amnesty ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Litinin.

Ta ce, “Ya zuwa yanzu, rundunar ‘yan sandan Nigeria ta kashe akalla mutane 10 tun bayan da aka fara zanga zangar kawo karshen rundunar SARS a kasar.

  Munirat Abdulsalam ta bayyana kasancewarta musulma

A ranar Asabar, kamar yadda rahotanni suka bayyana, ‘yan sanda a garin Ogbomosho, jihar Oyo, sun kashe wani matashi, Isiaq Jimoh, wanda ke cikin masu zanga zangar.

Zanga-Zangar tsige SARS

Bada dadewa ba hakan ta faru

A ranar Litinin kuwa, an sake kashe wani mai zanga zangar a yankin Surulere, jihar Lagos.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce zai tabbata an dauki mataki kan gurbatattun jami’an SARS, ba tare da nuna sani ko sabo ba.

  FG ta gabatar da manhajar UTAS kuma sun bayyana cewa suna dab da samun masalaha tsakaninsu da ASUU

Shugaban kasar ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja a yayin kaddamar da wani shirin shugaban kasa na mata, da zai samar da ayyuka ga matasa 774,000 a jihohi 36 na kasar.

Buhari ya kuma ce ruguza rundunar SARS, matakin farko ne na yin garambawul a rundunar ‘yan sandan Nigeria karkashin gwamnatin sa.

Zanga-Zangar tsige SARS

A wani labarin, Tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria, Atiku Abubakar, a ranar Lahadi ya jinjinawa matasan Nigeria bisa jajurcewarsu na yakar zaluncin da rundunar ‘yan sanda ke yi.

  Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sukai awon gaba da mutane 17 a jahar Nassarawa

Atiku, ya nuna gamsuwarsa, kan yadda matasan kasar suka hurawa rundunar ‘yan sanda wuta har sai da ta rushe sashen rundunar na FSARS da ke yaki da fashi da makami.

A cikin wata sanarwa daga hadiminsa ta fuskar watsa alabarai Paul Ibe a Abuja a ranar Lahadi, Mr Abubakar ya ce rushe SARS alama ce ta bin tsarin wadatar da ‘yan Nigeria ta fuskar tsaro.

Leave a Reply

Translate »