July 29, 2021

Chelsea: Babu wanda ze kara sa mana kwallo a raga-Lampard

2 min read
Chelsea

Chelsea ta amshi bakuncin takwararta ta Sheffield United a fafatawar su ta zama zakan gwajin dafi a firimiya lig.

Chelsea ta amshi bakuncin takwararta ta Sheffield United a fafatawar su ta zama zakan gwajin dafi a firimiya lig.

A jiyanne dai su mazauna birnin London Sun sami nasarar lallasa takwarar tasu da ci 4-1 da yammacin ranar.

Sheffield sun kasance da zafinsu tin daga farkon fara taka ledar har zuwa mintuna 20 na farko.

A cikin haka ne dai McGoldrick ya sami nasarar jefawa Chelsea kwallo ta farko a raga.

Babu wata damuwa daga yan wasan chelsea, kama daga kan me horar da yan wasa harda magoya bayansu.

Tsohon dan wasan tsakiyar na chelsea ya nuna godiyarsa karara da nuni da jin dadinsa ga nasarar da suka samu a wasan.

Chelsea fc. against Sheffield United

Lampard yayi nuni da cewa “kafin dariya akanyi kukan wahala” amma yanzu babu abinda bazamu iya yi ba a firimiy.

Tammy Abraham, Ben Cjilwill, Thiago Silva da Timo Werner su suka sami nasarar banbanta wasan da kwallo daya daga kafar kowannen su.

“Wannan shine alamar nasararmu a wasan Chanfiyon da duniya me zuwa bada dadewa ba” inji me horar da yan wasan chelsea.

Ziyetch shine dan wasan da yafi kowa motsi a yan wasan kusa da raga na Chelsea bayan da ya bayarda gudummuwa 4 zuwa biyar ga dukka yan wasan da suka ci kwallayen.

Chelsea sun buga wasannani 11 a gasa daban-daban ba tareda anyi nasara akansu ba kuma hakan ya basu damar tsallakawa gurbi na uku a tebur.

Daga wancen bangaren kuma McGoldrick da ya riga ya sanar da ritayar sa a satin shine ya sami nasarar jefa kwallon daya a ragar Cjelsea.

Sjeffield sun bata kimanin minti 30 bayan dawo wa hutun rabin lokaci suna komarin kare gida wanda haka ya ba yan gaban Chelsea damar zuba musu kwallayen.

  Chelsea 3-0 Rennes: Vote of thanks to all the Blues - Lampard

Leave a Reply

Translate »