August 2, 2021

Barista Bulama Bukarti yana bincike akan mafakar Boko haram ta Neja

2 min read
Barista Bulama

Barista Bulama Bukarti mai bincike kan ƙungiyoyin 'yan ta-da-ƙayar-baya a cibiyar Tony Blair Institute da ke Burtaniya ya ce

Barista Bulama Bukarti mai bincike kan ƙungiyoyin ‘yan ta-da-ƙayar-baya a cibiyar Tony Blair Institute da ke Burtaniya ya ce

Saƙon da Boko Haram da ta fitar inda aka ga wani mayaƙin ƙungiyar na bayyana kansa a matsayin kakakinta a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya babbar barazana ce ga tsaron ƙasar.

Sanin da akaiwa ƙungiyar shine ta fi ƙarfi ne a arewa-maso-gabashin ƙasar, tun bayan da tasirinta a wasu jihohin ƙasar ya ragu.

Sedai Bulama Bukarti, mai bincike kan ƙungiyoyi masu ta da ƙayar baya a cibiyar ta Tony Blair, ya bayyana wa BBC cewa idan ta tabbata ƙungiyar na da sansani a jihar Neja, za ta iya kai hari a Abuja da wasu jihohin da ke maƙwabtaka da ita.

Wani Bidiyo mai tsawon minti shida, wasu mayaƙan Boko Haram bakwai sun yi jawabai inda suke iƙirarin cewa suna aiko da saƙon ne daga sassa daban-daban.

  Karshen yan SARS ya kare a Najeriya

Dayawansu sun ce suna magana ne daga Kamaru da dajin Sambisa da kuma yankin tafkin Chadi.

Sedai  saƙon da ya fi jan hankali shi ne na mayaƙin da ya yi iƙirari cewa shi ne kakakin kungiyar kuma yana magana be ne daga jihar ta Neja.

Kowanensu ya fara da miƙa sakon gaisuwa ga shugabansu Abubakar Shekau, kuma sun yi barazanar kai wasu munanan hare-hare a kwanaki masu zuwa.

Shugaban binciken na ganin saƙon daga kungiyar Boko Haram yake:

“Tabbas wannan faifan bidiyo daga Boko Haram yake, wato bangaren Abubakar Shekau.

Amma ba mu tabbatar ko daga jihar Neja yake aiko da saƙon ba, ko kuwa a wani wuri na daban aka dauki bidiyon amma yake barazana, yana ƙarya cewa yana jihar Neja ne.”

  Yadda za'a shiga tsarin Tallafin NYIF da Nasal(NIRSAL) kai tsaye.

“Idan gaskiya ta tabbata cewa akwai mayaƙan Boko Haram a jihar Neja, to akwai hatsari mai matuƙar girma,” in ji Bulama Bukarti.

“Wannan Jiha ta Neja ita ce jiha ta biyu a girma ta ɓangaren fadin kasa a Najeriya, kuma tana da daji mai duhu da duwatsu masu yawa.

Sarkakiyarta ta shiga jihar Kaduna kuma ya haɗa da dazuzukan da ke jihohin Katsina da Zamfara har zuwa Sokoto.”

Barista Bukarti ta ce: “Da zarar mayaƙan Boko Haram suka yi karfi a dazukanta, to ba abu ne mai wuya ba su kai hare-hare babban birnin tarayyar Najeriya ba.”

Abun mamaki kuma shi ne na sabon salon da ƙungiyar ke amfani da shi wajen mika saƙonninta.

  Inna lillahi: Kimanin sojoji goma 'yan ta'adda suka kashe Najeriya yau dinnan

Lokutan  baya, shugabanta ne kawai aka sani yana magana da yawunta, amma sai yanzu aka ga wasu mayaƙanta na mika saƙonni a madadinta.

Shugaban binciken ya kara da cewa “Ina ganin matasa sun gane cewa shi Abubakar Shekau mutum ne wanda ba shi da tausayi, maras imani wanda ke da ƙishin kashe bayin Allah wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Lallai wannan sabuwar dabara ce da ƙungiyar ta fito da ita ta amfani da wasu muryoyi da fuskokin da matasa ba su saba da su ba – domin sun dawo daga rakiyar Abubakar Shekau.

Sannan ya kara da cewa  fatan Boko Haram shi ne ta yaudari matasa domin su shiga ƙungiyar.

Leave a Reply

Translate »