March 4, 2021

Atiku Abubakar yayi niyyar mayarda ‘ya-‘yan su 3 ga tsohuwar matarsa

1 min read
Atiku Abubakar

Atiku Abubakar yayi ikrarin zama da 'ya-'yan sa amma wata Babbar kotun Kubwa da ke birnin Abuja, ta umarci da yayi gaggawar mayar wa tsohuwar matarsa yaransu 3

Atiku Abubakar yayi ikrarin zama da ‘ya-‘yan sa amma wata Babbar kotun Kubwa da ke birnin Abuja, ta umarci da yayi gaggawar mayar wa tsohuwar matarsa yaransu 3 

Abubakar Atiku, da ne ga tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, dama ya kwace yaran 3 ne tun bayan rabuwarsu 

Alkali Mai shari’a, Bashir Danmaisule, ya ce Abubakar bai gabatar da hujjojin da za su hana Maryam Sherif rike yaranta ba 

  Yawancin mutanen da suka mutu sakamakon zanga-zangar EndSARS a jiya

Wata babbar kotu da ke Kubwa a Abuja, ta umarci Alhaji Atiku Abubakar da ya mayar wa Maryam Sherif, tsohuwar matarsa yaransu 3 da ke hannunsa take-yanke. 

  Nigeria: Gwamnati tayi zazzafan bincike bisa bannata kayan tallafin covid-19

A shekarar da ta gabata ne Maryam ta maka Abubakar kotu, inda take bukatar ya bata yaransu maza 3 da yake rike dasu. 

Abubakar da ne ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. 

Alkalin kotun, Bashir Danmaisule, ya ce Abubakar bai bayar da wata hajja a musulunce da za ta hana uwar amsar yaranta ba. 

  Karshen yan SARS ya kare a Najeriya

Amma zai iya daukaka kara cikin kwanaki 30. 

A kotun, Maryam da lauyanta, Nasir Sa’idu sun halarci zaman, yayin da Abubakar da lauyansa , Abdullahi Hassan kuwa basu je ba.

Leave a Reply

Translate »