ASUU: An ba hammata isja a taron kawo karshen yajin aiki da FG
1 min read
An tashi baram baram a zaman sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU.
ASUU sun gudanar da taro da An tashi baram baram a zaman sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar jamioin Najeriya
Kungiyar malaman jami’o’i da gwamnatin tarayya sun shiga ganawa a ranar Alhamis, da zummar kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta shiga.
Da farko, shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayar da haske kan cewar a shirye malaman jami’o’in su ke su koma koyarwa.
Ya bayar da tabbacin ne biyo bayan alkawarin da ministan kwadago da daukar aiki, Dr. Chris Ngige ya bayar a wajen taron, na cewar gwamnati za ta cika burin kungiyar.
Sai dai, a daren ranar Alhamis, gidan talabijin na TVC News, ya ruwaito cewa, an tashi baram baram a karshen taron, ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba.
A wani labarin, A ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara shirin ruguza hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da dangoginsu da suka hada da EFCC da kuma ICPC.
Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisar, mai taken: “Dokar hukumar gurbattun kudade”.